Hon. Nafi'u Roja Movement

Hon. Nafi'u Roja Movement Ku biyo ni a wannan shafi Please �

Cikin ikon Allah a yau Alhamis 27/3/2025Mai girma shugaban majalisar kansilolin ƙaramar hukumar Kumbotso RT. Hon Nafi'u ...
27/03/2025

Cikin ikon Allah a yau Alhamis 27/3/2025

Mai girma shugaban majalisar kansilolin ƙaramar hukumar Kumbotso RT. Hon Nafi'u Alhassan Roja Mariri ya jagoranci rabon tallafin kayan sallah ga Marayu a Mazaɓar sa ta Mariri wanda Ƙungiyar Marayu ta mariri take gabatarwa duk shekara ga marayun

Wannan tallafi dai an daɗe ana gabatarwa tsawon shekara da shekaru a karkashin jagorancin wannan ƙungiyya ta marayu wanda shima Hon Speaker yana ɗaya daga cikin committee wannan ƙungiya dake tallafawa marayu a duk shekara dama ko yaushe

Muna addu'ar Allah ya sakawa dukkanin waɗanda suke bada gudunmawar su ga wannan ƙungiya da alkhairi yasa a mizani

✍️ Sarkin Yaƙin Nafi'u Roja

Daga hawansa zuwa yau.....Mai grima kakakin majalisar kansiloli ta karamar hukumar kumbotso Hon Nafi'u A Roja  Kuma Zabb...
13/03/2025

Daga hawansa zuwa yau.....

Mai grima kakakin majalisar kansiloli ta karamar hukumar kumbotso Hon Nafi'u A Roja Kuma Zabbaben kansilan Mazabar Mariri,Wanda ya karbi rantsuwar k**a aiki ranar 27/10/2024.

A Matsayina na Kansila Kuma kakakin Kansilolin karamar hukumar yanada hakkin Al'umma a kansa k**a daga na ayyukan zahiri da Kuma badini(Intangible).Wanda a wannan watanni da ya dauka ya Samar da ayyukan kala kala Musamman ga Yan Mazabar sa ta Mariri ta fannoni daban daban.

Kadan daga cikinsu...

1. Kaddamar da aikin Kwalabati (drainage) a Unguwar Danladi Nasidi da ke Mariri.

2. Kaddamar da aikin Kwalabati ( drainage) a Danladi Nasidi Layin Massalacin Madina

3. Karasa aikin ginin block a Makarantar secondary ta Mata dake Mariri.

4. Gyara tare da inganta Ajujuwa a makarantar Primary ta Tsamiya Mariri.

5. Samar da Temporary office a Ofishin Hizba na Mariri.

6. Samarwa da Dalibai 57 gurbin karatu a makarantar Sa'adatu Rimi Wanda Mai Girma chairman na karamar hukumar ya dauki nauyi.

7. Raba litttafai ga Dalibai Yan primary.

8. Samar da kujeru Three seater a Makarantar Abdullahi Mariri.

9. Samar da Computer set ga hukumar Makarantar Abdullahi Mariri.

10. Samar da gurbin karatun a Makarantar koyon sana'oi ta Aliko Dangote ultra modern skills acquisitions Centre dake Zaria Road.

11. Raba katin Asibitin a Asibututuwan Mariri da Farawa

12. Samar da gurbin karatu a School of Nursing and Midwifery.

13. Taimakawa Islamiyyu da Tabarmi da kayan aiki ba yau da kullum.

14. Samar da Kyakyawan Tsarin wajen Tafiyar da shugabcin kasuwar Laraba da ke Mariri.

15. ya samar da Shaddodi da Atamfofi ga kungiyar Marayu ta Mariri.

16. Shine Kansila da ya kashe 3.5M wajen walwalar Al'ummarsa da Azumi.

17. Ya bayar da Taimakon 50,000 ga Masallacin yarabawa.

18. Ya bayar da Taimakon 50,000 ga wani Bawan Allah da za a yiwa aikin a Asibitin.

Bai tsaya nan domin ya mika sauran ayyuka ga shugaban karamar hukumar kumbotso Hon Abdullahi Ghali Basaf, wanda yake jiran sahalewarsu domin suna sauran gurare a waiwayi bukatar su

Wanda s**a hada da...

1. yin aikin Kwalabati daga Layin Marigayi Alanguburo zuwa Gidan Buredin Mama,Mariri.

2. Aikin Kwalabati a Unguwar Bare-Bari

3. Kewaye Asibitin Zara

4. Ginin makarantar Primary a Gadon Arewa

5. Aikin Solar layin Gidan Marigayi Alanguburo.

6. gyaran Asbiti a Gerawa Unguwar Farawa

7. Aikin Titin da ya hade sabuwar Zara da tsohuwa.

Ofishin Zabbaben kansilan Mariri Kuma kakakin Kansilolin karamar hukumar kumbotso, Hon Nafi'u Alhassan Roja.
✍️✍️✍️
12/3/2025

Aikin Alkhairi a jinin sa yake Allah ya kai matsayi gaba
10/03/2025

Aikin Alkhairi a jinin sa yake Allah ya kai matsayi gaba

Tallafin duba hamsin 50k ga wani bawan Allah da yake fama da cutar ciwon Cancer a Mazaɓar Kureken Sani Kamar yadda ya sa...
08/03/2025

Tallafin duba hamsin 50k ga wani bawan Allah da yake fama da cutar ciwon Cancer a Mazaɓar Kureken Sani

Kamar yadda ya saba bada tallafin sa a kowanne ɓangare dake faɗin karamar hukumar Kumbotso dama jahar Kano baki ɗaya a zahiri da kuma a ɓoye yauma 8/3/2025 cikin ikon Allah

Mai girma shugaban majalisar kansilolin ƙaramar hukumar Kumbotso RT. Hon Nafi'u Alhassan Roja Mariri ya baiwa wani bawan Allah mai suna Yayallo Magadawa daga mazaɓar kureken sani tallafin 50k domin ayi masa aikin cutar ciwon Cancer da yake fama dashi

Inda ya bada wannan tallafi ta hannun Alhaji Abubakar Garba Zaragoza wanda Sabiyola Magadawa ya karɓawa wannan mara lafiya tallafin

A madadin mai girma Speaker muna addu'ar Allah yasa ayi aiki lafiya ya bashi lafiya yasa kaffara shi kuma mai girma Speaker Allah ya saka masa da alkhairi yasa a mizani

✍️ Sarkin Yaƙin Nafi'u Roja

A ƙoƙarinsa na ganin ya tallafawa al'ummar ta kowanne ɓangare Hon Nafi'u A Roja Cikin ikon Allah a yau Asabar 8/3/2025 m...
08/03/2025

A ƙoƙarinsa na ganin ya tallafawa al'ummar ta kowanne ɓangare Hon Nafi'u A Roja

Cikin ikon Allah a yau Asabar 8/3/2025 mai girma shugaban majalisar kansilolin ƙaramar hukumar Kumbotso RT. Hon Nafi'u Alhassan Roja Mariri ya bada tallafin Naira Dubu Hamsin 50k ga Masallacin Yarabawa dake Mariri domin gudanar da wasu ƴan gyare-gyare a masallacin

Inda ya bada wannan saƙo ta hannun Alhaji Garba Zaragoza domin a miƙa su ga Committing wannan Masallaci

Muna addu'ar Allah ya saka masa da alkhairi 🤲 ya ƙara ƙarfin guiwa

✍️ Sarkin Yakin Nafi'u Roja

Address

Mariri
Kano
700104

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hon. Nafi'u Roja Movement posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hon. Nafi'u Roja Movement:

Share

Category