25/11/2025
SALLAR ASUBAH
Sallar Asubah haske ne ga ma'abota yin ta a kan lokaci masu fita a cikin duhu domin halartar sallarta, hakanan kuma bushara ce kamar yadda yazo a hadith.
Burayd Al-aslamy (RA) Ya ruwaito daga Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Ka yi albishir da cikakken haske ranar al-ƙiyamah ga masu fita zuwa masallaci domin sallar Asubah a cikin duhu.” [Abu-dawud da Tirmidhi s**a ruwaito, Albany ya inganta shi]
Wannan albishir ce ga masu sallar Asubah cikin jam'i masu halartar masallaci a cikin duhun asubah, duk wanda kuma yake son shiga cikin wannan bushara da Manzon ALLAH (ﷺ) yayi to sai ya jajirce wajen yin sallar Asubah a kan lokaci tare da halartar masallaci domin yin sallar acikin jam'i.
Allah bamu ikon kiyayewa